Annabi Muhammad Manzon Allah ne
Imani da sakon Annabi Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – shi ne bangare na biyu na ginshikin Musulunci, kuma babban asasin da aka gina shi a kansa.
Kuma mutum yana zama Musulmi ne bayan ya yi kalmar shahada tare da su, don haka ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ya shaida cewa lalle Muhammad Manzon Allah ne.
A- Menene ma’anar Manzo? Kuma wanene Muhammad? Shin akwai wasu manzanni banda shi?
Wannan shine abinda zamuyi ƙoƙarin amsawa a cikin waɗannan shafukan.
Manzo Mutum ne a mafi girman kololuwar gaskiya da kyawawan Halaye, Allah ya zabe shi daga cikin mutane, kuma ya bayyana masa duk abin da yake so na umarnin addini ko al’amura na gaibu da sauran al’amura don isar da su ga mutane. an banbanta da su daga wahayin da ya zo masa daga Allah, don haka ya sanar da shi game da Al’amuran gaibi da umarnin addini da yake isar da su ga mutane, haka nan kuma ya banbanta da su ta hanyar rashin kuskure Allah gare shi daga fadawa cikin manyan zunubai ko wani al’amari da ya keta isar da sakon Allah zuwa ga Mutane.
Zamu kawo wasu labaran manzannin da suka gabata kafin Annabi Muhammadu, SAW; Don ya bayyana mana cewa sakon Manzanni daya ne, wanda shi ne kira zuwa ga bautar Allah shi kadai, kuma za mu fara da yin bitar labarin farkon bil’adama da kuma kiyayyar Shaidan ga mahaifin ‘yan Adam, da zuriyarsa.