D- Annabi Musa, amincin Allah ya tabbata a gare shi
Daga nan wani sarki Azzalumi kuma mai girman kai ya tashi a Misira, ana kiransa Fir’auna, wanda yake da’awar allahntaka kuma yana umartar mutane da su bauta masa kuma su yanka wanda ya ga dama kuma su zalunci wanda ya ga dama, Allah madaukakin sarki ya bamu labarinsa da cewa:
Lalle ne Fir’auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama’a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir’auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
Sai mutãnen Fir’auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir’auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
Kuma matar Fir’auna ta ce (“Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã,” alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.
Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta. Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.
Kuma ta ce wa ‘yar’uwarsa, “Ki bĩ shi.” Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.
Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: “Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?”
Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa’adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: “Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!”
Ya ce: “Ya Uhangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara.” Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.
Ya ce: “Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni’imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba.”
Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, “Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne.”
To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce, “Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa.”
Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: “Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka.”
Sai ya fita daga gare ta, yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: “Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai.”
Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: “Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya.”
Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jama’ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: “Mẽne ne shã’aninku?” Suka ce, “Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho ne mai daraja.”
Sai ya shãyar musu, sa’an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa’an nan ya ce: “Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne.”
Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, “Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu.” To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: “Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai.”
¦ayarsu ta ce, “Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi amintacce.”
Ya ce: “Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan ‘yã’yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai.”
Ya ce: “Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa.”
To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, “Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi.”
To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) “Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu.”
“Kuma ka jẽfa sandarka.” To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. “Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu.”
“Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir’auna da ‘yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai.”
Ya ce: “Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni.”
“Kuma ɗan’uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni.”
Ya ce: “Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan’uwanka kuma Muka sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya.”
[Kasas: 4-35]
[1] Mahaifiyarsa ta saka shi a cikin akwatin gawa, ta jefa shi cikin Teku.
Sai annabi Musa da ɗan’uwansa annabi Haruna suka tafi zuwa ga Fir’auna – sarki mai girman kai – suna kiran sa zuwa ga bautar Allah, Ubangijin Talikai:
Fir’auna ya ce: “Kuma mene ne Ubangijin halittu?”
Ya ce: “Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni.”
Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, “Bã za ku saurãra ba?”
Ya ce: “Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.”
Ya ce: “Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne.”
Ya ce: “Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta.”
Ya ce: “Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru.”
Ya ce: “Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?”
Ya ce: “To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya.”
Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
(Fir’auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, “Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!
“Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?”
Suka ce: “Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan’uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne.”
“Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani.”
Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
Kuma aka ce wa mutãne “Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
“Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya.”
To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir’auna,”Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?”
Ya ce: “Na’am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai.”
Mũsã ya ce musu, “Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa.”
Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: “Da ƙarfin Fir’auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya.”
Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
Suka ce: “Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu.”
“Ubangijin Mũsa da Hãrũna.”
Ya ce: “Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya.”
Suka ce: “Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu.”
“Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni.”
Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne.
Sai Fir’auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
“Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan.”
“Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne.”
“Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne.”
Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
Da taskõki da mazauni mai kyau.
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
Sa’an nan a lõkacin da jama’a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: “Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne.”
Ya ce: “Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni.”
Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa “Ka dõki tẽku da sandarka.” Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
Sa’an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
[Shu’ara:: 23-67].
Lokacin da Fir’auna ya fahimci nutsewarsa ta zo sai ya ce: Na yi imani babu abin bautawa da gaskiya sai wanda Bani Isra’ila suka yi imani da shi, Allah Madaukaki ya ce:
Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?
To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.
Kuma Allah ya gadar wa mutanen (Musa) wadanda suke aka zalunta gabas da yamma na duniya, wadanda ya sanya wa albarka da halakar da abin da Fir’auna da mutanensa suka aikata da abin da suka gina.
Bayan haka, Allah ya saukarwa da wa Musa littafin Attaura, a ciki akwai shiriya ga mutane da haske wanda yake shiryar da su zuwa ga abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi, kuma a cikinsa akwai bayanin abin da yake halal da haram da cewa Bani Isra’ila (mutanen Musa) dole ne su bi.
Sannan annabi Musa, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya Mutu kuma Allah ya aiko annabawa da yawa a bayansa zuwa ga mutanensa – Banu Isra’ila – annabawan suna shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya duk lokacin da wani annabi ya rasu, sai kuma wani Annabin ya gaje shi.
Allah ya fada mana wasu daga cikinsu kamar annabi Dawud,annabi Sulaiman,annabi Ayyub da annabi Zakariya, kuma bai fada mana da yawa daga cikinsu ba. Sannan yacika wadannan Annabawan na banu Isra’ila da Isa Dan Maryam, amincin Allah ya tabbata a gare shi, wanda rayuwarsa ke cike da alamu tun daga haihuwarsa har zuwa hawansa zuwa sama.
Attaura da Allah ya saukar wa annabi Musa a kan tsararraki ta kasance cikin gurɓacewa da canzawa daga Hannun Yahudawa waɗanda suke da’awar cewa su mabiyan annabi Musa ne, amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuma annabi Musa barrantacce ne daga gare su, kuma Attaura da ke cikin hannayensu daga yanzu babu Attaura da aka saukar daga Allah, kamar yadda suka sanya a ciki abin da bai cancanci a ce wannan daga Allah yake, kuma suka siffanta Allah a ciki.da siffofi na tawaya, jahilci da rauni – Allah ya daukaka daga abin da suke ka ce – Allah Madaukaki Ya ce a cikin Bayanin su:
To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sannan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã’antãwa.
Baqara: 79