ADDININ GASKIYA

KAMAR YADDA AYOYIN ALKUR'ANI DA HADISAN FIYAYYEN HALITTA SUKA KAWO

Mai Karatu Maigirma

Wannan littafin, wanda ke Hannunka, ya gabatar maka da Addinin Musulunci, a saukakakkiyar Hanya wanda ya kunshi dukkan Bangarorinsa (imani – da’a – dokoki – da sauran koyarwarsa).

Anyi la’akari da Manyan abubuwa da yawa:

Na farko: Mayar da Hankali kan asalin abinda Addinin da ya ginu a kai.

Na Biyu, sanya shi gajere kamar yadda ya yiwu

Na Uku: Gabatar da Musulunci ta Hanyar Tushensa na Asali (Alkur’ani mai girma, Hadisan Manzo, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), don mai karatu ya tsaya fuska da fuska a gaban manyan mabubbugar Musulunci na asali da zai kwankwada kai tsaye shiriyarsa da koyarwarsa

Ya kai mai karatu, bayan ka kai karshen littafin, za ka ga cewa ka samar da cikakkiyar fahimta game da Addinin Musulunci, bayan haka kuma a hankali za ka iya kara daidaituwar ilimin game da wannan Addinin.

Wannan littafin da ke hHannunku abin sha’awa ne ga ga jama’a masu yawa, domin a matakin farko yana nufin wadanda ke son shiga Addinin Musulunci kuma su koyi abubuwan da yashafi imani da Allah, da ladubbansa da Hukunce-Hukuncensa.

Hakanan yana nufin wadan da suke da sha’awar koyo game da Addinai, musamman Addinan da miliyoyin Miliyoyin Mutane suka amince da su.Haka kuma yana nufin abokai na Musulunci da sukesuna da sassaukan ra’ayi game da Musulunci kuma suke jin daɗin wasu halayensa.Yana kuma nufin makiya da masu adawa da Musulunci. , wanda rashin sanin sa na iya zama ɗaya daga cikin manyan dalilan wannan ƙiyayya da waccan ƙiyayyar.

Wadanda suke da sha’awar wannan littafin su ne musulmin da suke son su bayyana Addinin Musulunci ga mutane.Wannan littafin yana takaita kokarinsu kuma yana saukaka musu himmarsu.

Kuma zaka iya samu, ya kai mai karatu, – idan baka da wata masaniya game da addinin musulinci – cewa kana bukatar dan maida hankali da karance-karance domin sanin ma’anonin da ke cikin wannan littafin, don haka kar ka gaji da hakan , kasancewar akwai wasu shafuka na musulinci wadanda suke amsa Tambayoyinka.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *