ADDININ GASKIYA

KAMAR YADDA AYOYIN ALKUR'ANI DA HADISAN FIYAYYEN HALITTA SUKA KAWO

D- Annabi Saleh, amincin Allah ya tabbata a gare shi

Sannan wani lokaci ya wuce sai kabilar Samudawa suka tashi a Arewacin yankin Larabawa kuma suka kauce daga shiriya kamar yadda wadanda suke a gabaninsu suka bata, sai Allah Ya aiko musu da wani Manzo daga cikinsu (Salih), amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuma ya goyi bayansa shi da aya mai nuna gaskiyar sa, kuma ita babbar rakuma ce wacce ba ta da kama da halittu, kuma Allah madaukaki ya ba mu labarinsa ya ce:

Kuma (muka tura) zuwa ga Samũdãwa ɗan’uwansu, Sãlihu, ya ce: “Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku.”

“Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni’imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi.”

Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, daga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: “Shin, kunã sanin cẽwa Sãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?” Suka ce: “Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne.”

Waɗanda suka yi girman kai suka ce: “Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne.”

Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: “Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa’adi da shi, idan kã kasance daga manzanni!”

Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne!

Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: “Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã isar muku da manzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!”

[Al-A’araf: 73-79].

Bayan haka, Allah ya aiko manzanni da yawa zuwa ga al’ummomin duniya, kuma babu wata al’umma da babu mai gargadi a cikinta. Allah ya bamu labarin wasu daga cikin su, kuma bai bamu labarin yawancin su ba, kuma dukkansu suna zuwa da sako guda daya ne, wanda yake umurtar mutane da su bautawa Allah shi kadai, wanda bashi da abokin tarayya, kuma su bar bautar wanin Allah. Allah yace:

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al’umma da wani Manzo (ya ce): “Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu.” To, daga gare su akwai wadanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sannan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.

Al-Nahl: 36

About The Author