ADDININ GASKIYA

KAMAR YADDA AYOYIN ALKUR'ANI DA HADISAN FIYAYYEN HALITTA SUKA KAWO

D- Annabi Hud, amincin Allah ya tabbata a gare shi

Sannan, bayan wani lokaci, sai Allah ya aika zuwa ga kabilar Adawa a wani yanki da ake kira Al-Ahqaf – bayan sun bata kuma sun bauta wa wanin Allah – sai ya aiko musu da wani manzo daga cikinsu, Hud, amincin Allah ya tabbata a gare shi .

Allah madaukakin sarki ya bamu labarin hakan da cewa:

Kuma (muka aika) zuwa ga Ãdãwa, ɗan’uwansu Hudu, ya ce: “Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?”

Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: “Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata.”

Ya ce: “Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!”

Inã isar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce.

“Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni’imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara.”

Suka ce: “Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa’adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya.”

Ya ce: “Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne.”

To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba.

[Al-A’araf: 65-72].

Sai Allah Ya saukar da wata iska a kansu a cikin kwanaki takwas, tana halaka kome da iznin Ubangijinta, kuma Allah Ya tserar da annabi Hudu da wadanda suka yi imani tare da shi.

About The Author