ADDININ GASKIYA

KAMAR YADDA AYOYIN ALKUR'ANI DA HADISAN FIYAYYEN HALITTA SUKA KAWO

B- Na farkon Manzanni, Babanmu Adam, amincin Allah ya tabbata a gare shi:

Allah ya halicci Babanmu Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi daga yumbu sannan kuma ya busa masa rai daga ruhinsa, Allah madaukaki ya ce

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sannan kuma Mun sũrantã ku, sannan kumaMun ce wa malã’iku: “Ku yi sujada ga Ãdam.” Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.

Ya ce: “Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?” Ya ce: “Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka.”

Ya ce: “To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci.”

Ya ce: “Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su.”

Ya ce: “Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri.”

A’araf: 10-15}

saboda haka Ya roki Allah da yabashi lokaci kuma kar ya hanzarta masa da Azaba kuma ya bashi damar Jarabtar Annabi Adam da zuriyarsa saboda Hassada da kiyayya gare su.Don haka Allah ya ba da izinin don wata hikima da yake so, mamayar Shaidan ta hanyar jarabar Adamu da zuriyarsa, ban da bayin Allah na gaskiya, kuma ya umarci Adamu da ‘ya’yansa kada su bauta wa Shaidan kuma kada su mika wuya ga jarabarsa kuma su nemi kariyar Allah daga gare shi Kuma jarabawar farko ta Shaidan ta fara ne ga Adam da matarsa Hauwa’u. Wanda Allah ya halitta daga hakarkarinsa) a cikin labarin da Allah madaukakin sarki ya ambata:

“Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga Azzãlumai.”

Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al’aurarsu, kuma ya ce: “Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciyar ba fãce dõmin kada ku kasance malã’iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama.”

Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.

Sai ya saukar da su da rũɗi. Sannan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al’aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: “Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?”

Suka ce: “Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.”

Ya ce: “Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi.”

Ya ce: “A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku.”

Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al’aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!

Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al’aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanya Shaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.

{Al-A’raf 19-27}

Kuma bayan da Adam ya sauko Duniya ya samar da ‘ya’ya da‘ Zuriya, ya mutu, amincin allah ya tabbata a gare shi, sannan zuriyarsa suka yawaita, zuriya zuwa zuriya, suka shiga jarabawar Shaidan, karkacewa ta bazu a tsakaninsu, da bautar kaburburan salihai da na iyayansu, kuma suka juya daga imani zuwa shirka, sai Allah Ya aiko musu da wani Manzo daga gare su (Nuhu, amincin allah ya tabbata a gare shi).

About The Author